Gwamnatin Zamfara ta bawa ma’aikata da ƴan fansho goron Sallah

0
193

Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da biyan kuɗin goron Sallah ga dukkan ma’aikatan gwamnati da kuma ‘yan fansho a jihar.

Wannan mataki na nuna ƙudurin gwamnan wajen tallafa wa jin daɗin al’umma, musamman a lokacin wannan babbar Sallah da take cike da ibada, tunani da kuma raba farin ciki da juna.

Kwamishinan yaɗa labarai da al’adu na jihar, Alhaji Mahmoud Muhammad Dantawasa, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, inda ya ce wannan kuɗi zai taimaka wajen rage wa iyalai nauyin rayuwa tare da ba su damar gudanar da bukukuwan Sallah cikin annashuwa.

A cikin sakon sa ga al’ummar jihar daga ƙasar Saudiyya inda yake gudanar da aikin Hajji, Gwamna Lawal yayi alheri tare da addu’o’i don yin bikin Sallah cikin zaman lafiya da farin ciki a jihar Zamfara.

Ya kuma yi kira ga dukkan mazauna jihar da su gudanar da bukukuwan Sallah cikin natsuwa, tare da ci gaba da saka jihar Zamfara cikin addu’o’insu domin samun zaman lafiya, ci gaba da wadata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here