Fitaccen attajirin duniya Bill Gates, yana shirin kawo ziyara ƙasar nan a mako mai zuwa.
A yayin wannan ziyarar, zai gana da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da wasu manyan jami’an gwamnatin tarayya.
Ziyarar za ta mai da hankali ne kan tattaunawa game da yadda za’a gyara tsarin kiwon lafiya a matakin farko.
Ana sa ran za a yi nazari kan hanyoyin inganta damar samun kiwon lafiya, gina ingantattun cibiyoyi, da kuma tabbatar da sakamako mai dorewa ga lafiyar al’umma a faɗin ƙasar nan.
A baya dai Bill Gates, ya bawa shugabannin Najeriya shawarar faɗaɗa tunanin su akan hanyoyin karɓar haraji, inda yace ba’a biyan haraji yadda ya kamata a Najeriya.