Ɗan daba ya mutu a ƙoƙarin kwacen waya a Kano—Civil Dafence

0
119

 Rundunar tsaron a’lumma ta farin kaya ta Civil Defence reshen jihar Kano ta fitar da sanarwa kan wani rikici da ya faru a unguwar Gwazaye, cikin ƙaramar hukumar Kumbotso, inda wasu da ake zargin ‘yan daba ne suka kai hari ofishin hukumar da ke yankin Semegu.

A cewar sanarwar da mai magana da yawun rundunar, SC Ibrahim Idris Abdullahi, ya fitar a yau, abin da ya faru ya samo asali ne daga wani yunkurin sace waya da wasu ‘yan daba biyu da ke dauke da wukake suka yi wa wani mazaunin yankin.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa ɗaya daga cikin barayin ya ƙwace waya daga hannun wani mutum amma sai mutumin ya mayar da martani ta hanyar kokarin karɓar wayar daga wajen ɗan daban, lamarin da ya haifar da faɗa har ya kai ɗan daban ya samu rauni a wuya kuma hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa.

Mutumin da aka kai wa harin tare da wasu makwabtan sa uku sun garzaya ofishin Civil Defence a Semegu domin kai rahoton lamarin. Sai dai daga bisani wasu mutane da ake zargin abokan wanda ya rasu ne, suka kai hari ofishin rundunar da makamai, bisa zargin cewa jami’an tsaron ne suka yi wa abokinsu illar data kashe shi.

Rundunar ta bayyana cewa babu wani jami’inta da ya shiga cikin wannan rikici.

Hukumar ta Civil Defence ta kuma tabbatar wa da al’umma cewa ba ta da hannu cikin kashe ko raunta wani ɗan daba a yankin. Don haka, lamarin yanzu yana hannun sashin binciken manyan laifuka na ‘yan sanda, domin gudanar da bincike mai zurfi da ɗaukar matakin da ya dace.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here