Ƴan siyasa ne ke rura wutar Boko Haram saboda a kayar da Tinubu—Orji Kalu

0
89

Tsohon Gwamnan Jihar Abia kuma Sanata mai wakiltar Abia ta Arewa, Orji Uzor Kalu, ya zargi wasu jiga-jigan ‘yan siyasa da hannu a harkar Boko Haram da nufin kifar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

A wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na tashar Channels TV a ranar Litinin, Kalu ya bayyana cewa sake farfadowar kungiyar Boko Haram yana da nasaba da siyasa, kuma wasu mutane masu neman mulki ne ke ƙulla hakan.

Ya ce yan siyasa ne ke bayan Boko Haram. Suna amfani da ta’addanci a matsayin makami don yakar Tinubu kamar yadda suka yi wa gwamnatocin da suka gabata.

Lokacin da aka tambaye shi su waye yake nufi da kalmar “jiga-jigan siyasa,” Kalu ya bayyana cewa yana nufin ‘yan siyasa, masu kudi, da manyan ma’aikatan gwamnati.

Ya ƙara da cewa siyasa ce ke haddasa rashin tsaro a Najeriya. Yan siyasa, ‘yan kasuwa, da manyan ma’aikata ba wai kuɗi kawai suke nema ba, sai dai suna ƙoƙarin kwace daga hannun Tinubu.

Wannan zargi na Kalu, yazo bayan kwana guda da samun rahotannin kashe mutane tara da aka ce Boko Haram ta hallaka ta hanyar fashewar bama-bamai a kauyen Mairari, ƙaramar hukumar Guzamala ta Jihar Borno.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here