Shugaban mulkin soji na Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani, ya zargi Najeriya tare da Faransa, China da Amurka da hannu a ayyukan ta’addanci da ke addabar ƙasarsa.
A wani jawabi na tsawon awa uku da ya gabatar kai tsaye a gidan talabijin na Radio-Télévision du Niger (RTN) a ƙarshen mako, Tchiani ya yi magana da harsuna uku, Hausa, Zabarma da Faransanci, inda ya bayyana cewa Najeriya, Jamhuriyar Benin, Faransa, China, Aljeriya da Amurka na ƙoƙarin jefa Nijar da sauran ƙasashen haɗakar AES cikin rudani.
Sabon zargin na zuwa bayan makamancin irin wannan zargi da ya yi a wata hira da aka yi da shi a ranar Kirsimeti ta shekarar da ta gabata, inda ya ce Faransa tana aiki tare da ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya a yankin tafkin Chadi domin kawo cikas ga tsaron Nijar, tare da sanin gwamnatin Najeriya.
Janar Tchiani ya bayyana cewa an gudanar da wata ganawa a asirce a Abuja a watan Disamba 2024, inda aka tsara yadda za a afka wa Nijar. A cewarsa, a watan Janairu 2025 kuma, wakilai daga Benin, Côte d’Ivoire da wasu ƙasashen yammacin Afirka sun sake yin taro a Abuja domin nazari da tsara sabbin dabarun kawo cikas ga Nijar, sai dai shirin bai yi nasara ba.
Zarge-zargen sun fito ne a daidai lokacin da ake fama da hare-haren ’yan bindiga a yankunan Tahoua da Dosso, inda aka kashe fiye da sojoji 100, lamarin da ya tayar da hankulan jama’a a fadin ƙasar.
A martanin da gwamnatin Najeriya ta fitar, ta musanta zargin baki ɗaya, tare da bayyana su a matsayin ƙage marasa tushe ko wata hujja mai karfi.