Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya jagoranci wata tawaga zuwa ƙananan hukumomin Nasarawa, Minjibir da Gwale domin yin ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a wani haɗarin mota bayan sun wakilci Jihar Kano a gasar wasanni ta ƙasa da aka gudanar a Jihar Ogun.
Mataimakin Gwamnan ya cika alkawarin baiwa kowa daga cikin iyalan mamatan naira miliyan ɗaya, tare da raba kayan abinci da suka haɗa da shinkafa, taliya, man girki, da garin tuwo domin tallafa musu.
Tawagar da ta raka Mataimakin Gwamnan sun haɗa da Sakataren Gwamnatin Jihar Kano da shugabannin ƙananan hukumomin Nasarawa da Minjibir.
Mutanen da suka rasu su 22 sun kasance wakilan jihar Kano a gasar wasanni ta ƙasa data gudana a jihar Ogun.