Kungiyar Ma’aikatan shari’a ta ƙasa (JUSUN) ta fara yajin aiki a yau Litinin, inda ma’aikatan reshen Kotun tarayya suka toshe ƙofofin shiga kotun, tare da hana alkalai, lauyoyi, ma’aikata da masu shari’a shiga harabar kotun.
Wannan yajin aiki ya biyo bayan sanarwar da ƙungiyar JUSUN ta ƙasa ta fitar, akan gazawar gwamnati wajen aiwatar da tsarin sabon mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000 da kuma biyan alawus.
An hana shiga kotunan ga alkalai, ma’aikata, lauyoyi, masu shari’a da sauran jama’a, lamarin da ya sa harkokin shari’a suka tsaya cak a harabar kotuna.
A hedkwatar Kotun tarayya da ke kan titin Shehu Shagari a birnin Abuja, an rufe dukkan ƙofofin shiga ginin kotun.
Kotun Ɗaukaka Ƙara da kuma Babbar Kotun Abuja (FCT High Court) da ke Maitama suma an rufe su.
A ranar 30 ga Mayu, ƙungiyar ta ƙasa ta JUSUN ta fitar da wata sanarwa da sakataren riƙo na ƙasa, M.J. Akwashiki, ya sanya wa hannu, inda ta umarci shugabannin ta na sassan Najeriya su umurci mambobinsu da su zauna a gida daga ƙarfe 12 na dare ranar Lahadi, 1 ga Yuni.
Sai dai ma’aikatan shari’a da ke ƙarƙashin hukumar Shari’a ta Ƙasa (NJC) da kuma na Kotun Koli ba su shiga yajin aikin ba, kamar yadda Joel Ebiloma, mai magana da yawun JUSUN, da Danladi Nda, shugaban reshen Kotun Koli na JUSUN, suka bayyana a karshen mako cewa ba za su shiga yajin aikin ba.