Al’ummar wasu kauyuka a karamar hukumar Maru da ke jihar Zamfara sun bayyana cewa mutane akalla 20 sun rasa rayukansu a wani hari da ‘yan bindiga suka kai, tare da farmakin da wani jirgin saman sojoji ya kai domin fatattakar ‘yan ta’addan.
Wani mazaunin yankin ya shaida wa BBC, cewa ‘yan bindigar sun sace fiye da mutane 50 da ke aikin noma, kafin daga bisani jirgin soji ya iso domin kai dauki.
Sai dai mazauna yankin sun ce maimakon jirgin ya kai dauki, sai ya bude wuta kan wasu daga cikin ‘yan sa-kai da suka fito domin kare mutanen yankin.
A cewar mazauna kauyen Mani da ke yankin Maru, ‘yan bindigar da ke kan babura sun kai harin da rana, a daidai lokacin da mutane ke aikin noma.
“Da zuwan ‘yan bindigar, sai suka fara harbin kan mai uwa da wabi tare da kama wasu daga cikin manoman,” in ji wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa.
Ya ce yayin da su ke kan hanyarsu ta zuwa kai dauki ga wadanda aka kai wa harin, sai suka hango jirgin saman sojin yana sauka. “Maimakon ya kai mana dauki, sai ya fara harbe mu. Muna ta gudu don tsira da rayukanmu,” in ji shi.
Wani mazaunin kauyen ya bukaci gwamnatin tarayya da ta turo karin jami’an tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a. Ya ce ‘yan bindigar sun yi barazanar dawowa garuruwan da suka kai wa hari.