Gwamnatin tarayya ta bayar da hutun babbar Sallah
Gwamnatin tarayya ta ayyana Juma’a, 6 ga Yuni, da Litinin, 9 ga Yuni, 2025, a matsayin ranakun hutu domin bikin Sallah Babba (Eid-ul-Adha).
Ministan harkokin cikin gida Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya sanar da hakan, inda ya mika sakon taya murna ga daukacin Musulmin Najeriya da na duniya baki daya dangane da zuwan Sallar.
Tunji-Ojo ya bukaci Musulmai da su kiyaye darussan da ke cikin hadayar Annabi Ibrahim (A.S) wato sadaukarwa, biyayya, da kuma nuna gaskiya a yayin bukukuwan Sallar babba.
Haka kuma, ya shawarci ‘yan kasa da su yi amfani da wannan lokaci na bukukuwa wajen rokon Allah da addu’o’i don samun zaman lafiya, hadin kai da ci gaban Najeriya.