Ɗan majalisar wakilai na ƙaramar hukumar Bichi, ya yi ta’aziyyar rasuwar ƴan wasan Kano

0
66

Ɗan majalisar wakilai na ƙaramar hukumar Bichi, ya yi ta’aziyyar rasuwar ƴan wasan Kano

Ɗan majalisar wakilai na ƙaramar hukumar Bichi, Hon. Abubakar Kabir Abubakar, ya miƙa saƙon ta’aziyyar sa akan faruwar hatsarin da yayi sanadiyar mutuwar mutane 22 ƴan jihar Kano.

Hakika na kadu da samun labarin rasuwar ‘yan wasa 22 daga cikin tawagar jihar Kano da ta halarci gasar wasanni ta kasa (National Sports Festival) wanda ta gudana a jihar Ogun sakamakon hatsarin mota, inji ɗan majalisar

Hatsarin motar ya ritsa da su ne a garin Dakatsalle a hanyarsu ta dawowa gida bayan kammala gasar.

Hon. Abubakar yace wannnan babban rashi ne ga jihar Kano da hukumomin wasanni na gida da kuma na Najeriya baki daya.

‘yan wasan sun rasu ne a daidai lokacin da wannan kasar ke bukatarsu sakamakon irin gudun mawar da su ke badawa don habaka harkokin wasanni a Najeriya.

Ya yiwa ‘yan uwa da abokanan arzuki da kuma hukumar wasananni ta jihar kano ta’aziyya wannan rashi.

Daga karshe yayi rokon Allah subhannahu wa ta’ala da ya ji kansu ya kuma bawa ‘yan uwansu juriyar wannan rashi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here