Attajirin Afrika Aliko Dangote, ya bayyana cewa ’yan Najeriya na biyan kashi 55 cikin dari ne kawai na farashin da ’yan wasu kasashen yammacin Afirka ke biya wajen siyan man fetur.
Dangote ya bayyana haka ne yayin wata ziyara ta musamman da shugaban kungiyar haɓɓaka tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS, Dr. Omar Touray, ya kai zuwa matatar mai ta Dangote da ke Legas.
Ya ce, fara aikin da matatar man sa tayi ta taimaka wajen rage farashin fetur a Najeriya.
A cewarsa, matatar na sayar da fetur tsakanin Naira 815 zuwa Naira 820 akan kowace lita, wanda hakan ya taimaka wajen daidaita farashin sa a kasuwa, duk da cewa ana samun canje-canje da hauhawar farashin mai a duniya.
Dangote ya kara da cewa Afrika za ta amfana matuka idan aka karfafa kasuwanci da cinikayya tsakanin kasashen nahiyar, inda ya jaddada yadda matatar tasa ke taimakawa wajen rage farashin kayayyakin da ake sarrafawa a Najeriya.