Mataimakiyar Gwamnan Jihar Ogun, Noimot Salako-Oyedele, ta sauka a jihar Kano, don jajantawa al’umma rashin waɗanda suka wakilci jihar Kano a gasar wasanni ta ƙasa data gudana a jihar Ogun.
Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, ne ya karɓi baƙuncin Noimot, da yan tawagar ta, bayan sun sauka a filin tashi da saukar jiragen sama na Malam Aminu Kano.
Idan za’a iya tunawa dai a jiya Asabar ne motar tawagar data wakilci jihar Kano a gasar wasanni ta ƙasa da aka gudanar a jihar Ogun ta gamu da hatsari a hanyar su ta dawowa gida, wanda hakan yayi sanadiyar mutuwar mutane 22, tare da jikkata wasu da dama.
Tuni gwamnatin Kano ta sanar da bayar da tallafin Naira miliyan 1 ga iyalan kowanne daga cikin waɗanda suka rasu, tare da ayyana Litinin a matsayin ranar hutu don jimamin rasuwar ƴan tawagar.