Sarkin Ƙaraye ne zai jagoranci kwamitin gudanar da Hajjin bana—Gwamna Abba

0
95

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya nada Mai Martaba Sarkin Karaye, Alhaji Dr. Muhammad Mahraz Karaye, a matsayin shugaban zai jagorantar kwamitin gudanar da aikin hajjin 2025 daga jihar.

Bayanin hakan na cikin wata sanarwa da Sulaiman A. Dederi, ya fitar, inda ya bayyana cewa kwamitin zai kasance cibiyar tsarawa da sa ido kan dukkan harkokin aikin hajjin bana daga farko zuwa ƙarshe.

Gwamnan ya ce an zaɓi Sarkin Karaye don jagorantar wannan tawaga domin tabbatar da ingantaccen tsarin gudanar da aikin hajji ga alhazai ‘yan asalin jihar Kano.

Mambobin kwamitin sun haɗa da:

Hon. Sarki Aliyu Daneji, ɗan majalisar dokokin mai wakiltar ƙaramar hukumar birni

Kwamishinan Harkokin Addinai, Sheikh Tijjani Auwal

Kwamandan Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Sheikh Tijjani Bala Kalarawi

Sheikh Dr. Bashir Aliyu Umar

Dr. Al-Fatihi Karbullah

Alhaji Yusuf Lawan

Sheikh Isma’il Ilyasu Mangu

Sheikh Tijjani Sani Maihula

Alhaji Abdullahi Kabir Yusuf

Hajiya Aisha Munnir Matawalle

Sheikh Basheer Arabi

Sakataren kwamitin shi ne Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa.

Wasu daga cikin waɗanda aka naɗa domin gudanar da aikace-aikace sun haɗar da;

Alhaji Yusuf Aliyu Muktar

Alhaji Muhammad Ghali Muhammad

Alhaji Umar Yakubu Kabara

Alhaji Murtala Lawan Sani

Hajiya Kubura Ibrahim Dankani

Hajiya Batulu Isa Waziri

Alhaji Abdullahi Muhammad Indabawa

Alhaji Hussani Abdul Inuwa

Gwamna Yusuf ya ja hankalin mambobin kwamitin da su gudanar da aikinsu da cikakken ƙwazo, gaskiya da rikon amana, yana mai roƙon Allah yasa ayi aikin hajji karɓaɓɓe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here