Na faɗa wa Tinubu ba zan zaɓe shi ba— Amaechi

0
145
Bola Ahmed Tinubu
Bola Ahmed Tinubu

Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa tun farkon fara yakin neman zaɓe kafin zaɓen 2023, ya shaida wa Shugaban ƙasa Bola Tinubu cewa ba zai goyi bayansa ko kada masa ƙuri’a ba.

Amaechi ya ce ya tsaya a kan maganarsa, inda bai yi aiki ko nuna goyon baya ga Tinubu ba, saboda a cewarsa Shugaban ƙasar ba shi da ƙwarewar shugabanci data dace da  Najeriya.

Ya bayyana haka ne yayin wata lacca da aka gudanar a Abuja ranar Asabar domin bikin cikar sa shekaru 60 a duniya.

Na shaida wa Tinubu a Yola, cewa ba zan goyi bayanka ba, ba zan yi maka aiki ba, inji Ameachi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here