Kungiyar matasan Tijjaniyya tayi alhinin rasuwar ƴan tawagar wasanni ta jihar Kano

0
85

Ƙungiyar wayar da kan matasan Tijjaniyya ta ƙasa ta bayyana rasuwar mutum ashirin da biyu daga cikin tawagar jihar Kano a gasar wasanni ta ƙasa da aka gudanar a Jihar Ogun a matsayin babban rashi ga ƙasa baki ɗaya.

Bayanin hakan na  cikin wata sanarwa da sakataren ƙasa na ƙungiyar, Shehu Tasiu Ishaq, da sakataren yaɗa labarai na ƙasa, Abubakar Balarabe Kofar Na’isa, suka sanyawa hannu.

Ƙungiyar matasan Tijāniyyar ta kuma aika da saƙon ta’aziyya ga gwamnatin jihar Kano, Mai Martaba Sarkin Kano, da kuma iyalan waɗanda abin ya shafa.

Ƙungiyar matasan Tijāniyya ta roƙi Allah Madaukakin Sarki ya jikan ‘yan wasan da suka rasu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here