Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana ranakun hutun Babbar Sallah ga dukkan makarantun Firamare da Sakandare da ke fadin jihar.
A cewar wata sanarwa da Daraktan Wayar da Kan Jama’a na Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano, Balarabe Abdullahi Kiru ya fitar a yau, hutun zai fara daga ranar Laraba, 4 ga Yuni, 2025.
Sanarwar ta bayyana cewa hutun zai kasance daga ranar Laraba, 4 ga Yuni, zuwa Lahadi, 15 ga Yuni, 2025 ga ɗaliban da ke zaune a makarantun kwana, yayin da ɗaliban da ke yin jeka ka dawo za su koma a ranar Litinin, 16 ga Yuni, 2025.
Gwamnatin ta bukaci iyaye da masu kula da ɗalibai da su je su ɗauki ‘ya’yansu daga makarantun kwana a ranar Laraba, 4 ga Yuni.
Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Dr. Ali Haruna Makoda, ya yi kira ga iyaye da su tabbatar da cewa ‘ya’yansu sun koma makaranta a ranar da aka tsara. Ya kuma gode musu bisa goyon baya da hadin kai da suke ci gaba da nunawa Ma’aikatar Ilimi ta jihar.