Gwamnan Ogun ya bayar da Naira miliyan ɗaya ga  iyalan ƴan wasan Kano da suka rasu

0
174

Gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya bayar da kyautar Naira miliyan ɗaya ga kowanne Iyalan ƴan wasan Kano da suka rasa rayukansu a hatsarin mota, yayin da suke dawowa daga gasar wasanni ta kasa ta National Sports Festival.

Wakilai daga Jihar Ogun, karkashin jagorancin Mataimakiyar Gwamna, Injiniya Noimot Salako-Oyedele, ne suka bayar da gudummawar kuɗin a ranar Lahadi. 

Cikin tawagar har da Sakataren Gwamnatin Jihar, Tokunbo Talabi, Kwamishinan Wasanni, Wasiu Isiaka; da Sakatare Janar na Kwamitin Shirya Gasar (LOC), Dr. Kweku Tandoh.

Tawagar ta kai ziyara Jihar Kano domin mika sakon ta’aziyya a madadin gwamnan jihar, wanda ke gudanar da aikin Hajji a halin yanzu. 

Haka kuma, sun jinjina wa jami’an ceto da suka hanzarta kai dauki ga waɗanda lamarin ya rutsa dasu, tare da yin addu’ar samun sauƙi ga wadanda ke jinya.

Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Kwamared Aminu Abdusalam Gwarzo, ne ya tarbi tawagar, tare da nuna godiya bisa wannan tallafi da jajantawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here