Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ayyana Litinin, 2 ga Yuni, 2025, a matsayin ranar hutu domin girmama matasa ‘yan wasa da jami’an wasanni 22 da suka rasa rayukansu a wani mummunan hadarin mota a hanyar su ta dawowa Kano daga Gasar Wasannin Kasa.
Sanarwar hutun ta fito a ranar Asabar ta hannun mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, wanda ya tabbatar da cewa hadarin ya faru ne a hanyar Kano–Zariya, inda wasu da dama suka samu munanan raunuka.
Wadanda suka rasu sun kasance cikin tawagar Jihar Kano da ta halarci Gasar Wasannin Kasa da aka kammala kwanan nan. Sun haɗa da ‘yan wasa, masu horaswa, da jami’an gwamnati da suka wakilci jihar a fannonin wasanni daban-daban.
Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda yake a kasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajji ya bayyana alhini da jimami matuƙa game da wannan rashi. Ya ce wannan lamari ya kasance daya daga cikin lokutan baƙin ciki da zafi a tarihin jihar.
An ayyana ranar hutun ne domin baiwa al’umma damar yin jimami, da kuma addu’a ga wadanda suka rasu. An kuma bukaci mazauna jihar da su yi addu’a tare da nuna tausayawa ga iyalan wadanda lamarin ya shafa.
Gwamnatin jihar ta bayyana cewa tana daukar matakai domin tallafa wa wadanda lamarin ya shafa, tare da kira ga shugabannin addinai da al’ummar Musulmi da su ci gaba da addu’a ga mamatan da kuma iyalansu.