Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya shawarci masu fafutukar siyasa da ke rike da madafun iko da su zama abin koyi ga jama’a, tare da kasancewa masu ɗaukar nauyin al’ummar da suka basu amana, da kuma kishin kasa.
Gwamna Uba Sani ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da wani littafi da Hon. Abdul Oroh ya rubuta mai suna: “Demonstration of Craze: Struggles And Transition To Democracy.”
A yayin da ya wakilci gwamnan wajen taron, Sakataren Musamman na Gwamna, Farfesa Bello Ayuba, ya ce masu fafutuka suna da nauyin hadin gwiwa wajen kare dimokuraɗiyya.