Wani mahaifi ya suma bayan matarsa ta haifi yara ’yan uku

0
63

Wani abin ban mamaki ya faru a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Tarayya dake Lokoja, jihar Kogi, a ranar Juma’a, inda wani mutum da aka bayyana sunansa da Adamu Muhammed Tenimu ya suma bayan an shaida masa cewa matarsa ta haifi ’yan uku.

Mutanen da abin ya faru a gaban idon su sun ce a lokacin da Adamu ya ji cewa matarsa ta haifi ’yan uku, ya cika da mamaki da farin ciki har ya fadi ya suma.

Ma’aikatan asibitin sun hanzarta taimaka masa, inda suka bashi kulawar da ya farfado cikin kankanin lokaci, sannan an bayyana cewa mahaifiyar da jariran na cikin koshin lafiya.

Da yake magana da manema labarai bayan ya farfado, Adamu, wanda ke cikin neman aikin yi, ya bayyana murna da kuma damuwa bisa rashin isassun kuɗi domin kula da jariran.

“Na gode wa Allah bisa wannan babban alheri, amma ina cikin ruɗani da bakin ciki. Ban san cewa ’yan uku muke dauke da su ba. A yanzu haka, ba mu da ikon biyan kuɗin asibiti balle mu kula da jarirai uku lokaci guda,” kamar yadda ya faɗa a cikin kuka.

Ya kara da cewa sun yi shiri don haihuwar jariri ɗaya saboda karancin kuɗi.

“Wannan ni’ima ce babba, amma nauyinta ma babba ne. Ko kuɗin sayen pampers ko abincin jarirai bani da shi. Ban san ta inda zan fara ba,” in ji Adamu

Wani dan uwa nna ya ce “Jariran suna cikin koshin lafiya, amma wannan iyali na bukatar taimako. Muna kira ga gwamnati, kungiyoyin agaji, kungiyoyin addini da dukkan ‘yan Najeriya masu zuciya ta alheri da su taimaka, a cewar mahaifin ƴan uku.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here