Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana alhininsa bayan samun labarin rasuwar Yan wasan da suka wakilci jihar Kano a Gasar wasanni ta kasa da aka gudanar a garin Abekuota dake jihar Ogun.
A yau Asabar da rana ne aka samu faruwar hatsarin motor data kwaso yan wasan tare da rasuwar mutane 21.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana rasuwar matasan da cewa wani babban rashi ne bawai ga iyalansu ba harma da al’ummar jihar Kano baki daya.
Sakataren yaɗa labaran Sarkin, Abubakar Balarabe Kofar Na’isa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwar daya fitar.
Sanarwar tace Alhaji Aminu Ado Bayero, yayi addu’ar Allah ya jikansu ya gafarta musu ya muma bawa iyalansu hakurin jure wannan babban rashi yasa aljanna ce makoma a garesu, tare da neman sauki ga waɗanda suka ji rauni.