Ganduje ya miƙa saƙon ta’aziyyar rasuwar matasan da suka wakilci Kano a gasar wasanni ta ƙasa

0
127
Gwamna Ganduje
Gwamna Ganduje

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, CON, ya bayyana alhininsa kan mummunan haɗarin motar da ya yi sanadin rasuwar ‘yan wasa 21 ‘yan asalin jihar Kano, yayin da suke dawowa daga gasar National Sports Festival da aka gudanar a Abeokuta, Jihar Ogun.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Edwin Olofu, ya fitar, Ganduje ya bayyana lamarin a matsayin babbar masifa mai tayar da hankali wadda ba ta girgiza mutanen Najeriya baki ɗaya.

Ya bayyana ‘yan wasan da suka rasu a matsayin matasa masu hazaka da kwazo, waɗanda suke wakiltar makomar wasanni a Najeriya da alfaharin jihar Kano.

Wannan lokaci ne na bakin ciki mai girma. Waɗannan matasan sun rasu cikin kishin ƙasa da ƙwazo domin wakiltar jiharmu, inji Ganduje. 

Shugaban APC na kasa ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda abin ya shafa, Jihar Kano, da kuma daukacin al’ummar masu sha’awar wasanni a Najeriya.

Ya kuma yi addu’a domin Allah ya jikansu ya kuma bai wa iyalansu da abokan arziki hakuri da karfin zuciya don jure wannan babban rashi, tare da yin addu’a Allah ya jikan mamatan ya kuma bawa waɗanda suka jikkata lafiya.

Ganduje, wanda ke gudanar da aikin Hajji a kasar Saudiyya a halin yanzu, ya kuma bukaci hukumomi su gudanar da cikakken bincike game da musabbabin hatsarin tare da daukar matakan kariya domin tabbatar da lafiyar ‘yan wasa da sauran al’umma a nan gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here