Mansurah Isah Ta Bayyana Rushewar Aurenta Na Biyu: ‘Na Yi Aure Ne Saboda Soyayya, Amma Shi Da Wata Manufa Ya Zo’

0
293

Fitacciyar jarumar masana’antar Kannywood, Mansurah Isah, ta tabbatar da rushewar aurenta na biyu, wanda ta bayyana a matsayin wani abu da ya faru cikin ba-zata, tamkar almara.

Mansurah ta ce ta shiga wannan auren ne bisa soyayya ta gaskiya, domin a cewarta, “so makaho ne”, amma daga bisani ta fahimci cewa mijin da ta aura ya zo da wata manufa daban, ba don soyayya da aure na hakika ba.

Ta bayyana haka ne a cikin shirin Mahangar Zamani na BBC Hausa, yayin wata tattaunawa da ita tare da tsohuwar jaruma Fati Mohammad, kan zargin da ake wa ’yan fim mata na Kannywood da rashin zaman aure mai ɗorewa.

A nata bangaren, Fati Mohammad ta ce mutane da dama suna yi musu gurguwar fahimta. Ta ce, “Aure ai yana da rai. Idan Allah ya kaddara ƙarshensa, to dole sai ya ƙare. Mutane da dama aurensu yana mutuwa, amma saboda ba a sansu ba, shi ya sa ba a jin labarinsu.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here