Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa INEC ta fara shirin yin amfani da ƙirƙirarriyar basira wajen gudanar da ayyukan ta.
Kwamishinan hukumar na ɓangaren yaɗa labarai da wayar da kai, Sam Olumekun, ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwar da ya fitar, inda yace fasahar za ta taimaka wajen sauƙaƙa wa hukumar ɗaukar matakai la’akari da bayanan da za ta samu ta hanyar fasahar AI.
Sanarwar ta ƙara da cewa fasahar zata taimaka wajen inganta harkokin zaɓe da yin sahihin zaɓe, musamman wajen tantance alƙaluman zaɓe.
Tuni dai hukumar ta sanar da kafa sashin fasahar ƙirƙirarriyar basirar ta AI a ƙarƙashin ɓangaren sadarwar hukumar, domin fara inganta ayyukan fasaha na hukumar, tare da kawar da matsalolin da ake fuskanta da suka shafi fasahar sadarwa.
Hukumar ta ce a baya-bayan nan ta halarci tarukan duniya waɗanda ta ce an shirya kan tasirin fasahar AI kan zaɓukan ƙasashen duniya.