Gwamnatin tarayya ta shigar da kara akan zargin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, da ɓata suna ta hanyar yin amfani da kafafen yada labarai na talbijin.
Sanata Natasha, dai itace ke wakiltar mazaɓar Kogi ta tsakiya a majalisar dattawa, kafin a dakatar da ita.
Gwamnatin tarayyar na zargin Natasha da aikata laifin ƙage, duk da cewa hakan ya saɓawa sashi na 392, na kundin tsarin mulkin ƙasa.
Daga cikin mutanen da gwamnatin ta sanya a matsayin shaidun da za su tabbatar da zargin, akwai Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, wanda Natasha ta zarga da neman aikata lalata da ita, da kuma tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.
Ɗaya ɗaga cikin zargin da gwamnatin ke yi wa Sanata Natasha shi ne inda ta zargi Godswill Akpabio da Yahaya Bello da yunƙurin shirya yadda za’a kashe ta.
A farkon watan Maris ne da Majalisar dattawa ta dakatar da ita tsawon wata shida bisa shawarwarin da kwamitin Ladabtarwa da Sauraron ƙorafin Jama’a na majalisar ya bayar, bayan nazari kan ƙorafin da Sanata Natasha ta miƙa wa majalisar dangane da zargin keta mata haddi daga shugaban majalisar.