Shugaban ƙasa Tinubu ya aikawa majalisun dokokin ƙasa buƙata amincewa kasafin kuɗin jihar Rivers na shekarar 2025, da yawan sa yakai Naira triliyan 1.481.
Kakakin majalisar wakilai Tajuddeen Abbas, ne ya bayyana hakan a zaman majalisar na yau Alhamis, yayin da ya karanto wasikar da shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya aike musu.
Wasikar tace za’a kashe Naira biliyan 324 wajen yin ayyukan gina kasa, sai Naira biliyan 166 da aka warewa fannin lafiya, da biliyan 75.6 ga fannin ilimi sai biliyan 31.4, ga fannin Noma.
Hakan dai ya biyo bayan aiwatar da dokar ta ɓacin da shugaban kasar yayi a Rivers, bayan dakatar da gwamnan jihar Siminalaya Fubara, a ranar 18 ga watan Maris na shekarar 2025, tare da sanya Ibok Ibas, a matsayin mai riƙon ƙwarya.