An fara shigar da kayan agaji zuwa yankin Gaza da yaƙi ya ɗaiɗaita.
Tuni dai manyan motoci ɗauke da kayan agaji, irin su fulawa suka fara shiga Zirin na Gaza ta mashigar Kerem Shalom bayan mako 11 da Isra’ila ta yi tana hana shigar da agaji yankin.
Majalisar Dinkin Duniya da shirin samar da Abinci na Majalisar sun ce a ranar Laraba an shigar da motoci aƙalla 90, wadanda a yanzu suka isa wuraren ajiyar abinci, inda kuma aka kai fulawar gidajen burodi.
BBC tace gefe guda kuma Isra’ila ta ci gaba da kai hare-hare a cikin dare, tare da kashe aƙalla mutum 10 a tsakiyar Gaza.
Sojojin Isra’ila sun ce bayar da umarni ga mazauna wurare 14 a arewacin Gaza, ciki har da Beit Lahia da Jabalia su tashi daga wuraren.