Kungiyoyin asiri sun janyo mana asarar Dala biliyan 1 a kowacce shekara—Gwamnan Edo

0
477

Gwamnan Edo, Monday Okpebholo, ya bayyana cewa jiharsa tana yin asarar sama da dala biliyan 1, da za’a iya saka ta a matsayin hannun jari a kowace  shekara sakamakon mummunan tasirin kungiyar asiri da tashe-tashen hankula masu nasaba da kungiyar asiri. 

Okpebholo, ya bayyana hakan a birnin Benin a ranar Laraba, yana mai cewa ayyukan kungiyoyin asiri na janyo koma baya wajen samun masu zuwa Edo don yawon bude ido, da asarar rayuka, wanda hakan ke lalata tattalin arziki.

Ya yi nuni da cewa, yawaitar tashe-tashen hankula masu nasaba da kungiyoyin asiri a cikin shekaru biyar da suka gabata ya haifar da cikas ga harkokin tattalin arziki, yayin da masu zuba jari da ‘yan kasuwa ke kara jan jiki daga Edo  saboda matsalar tsaro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here