Jami’an tsaron dake kare lafiyar gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum, sun wuta akan mayaƙan Boko Haram, yayin da gwamnan ke kan hanyar sa ta komawa Maiduguri daga Gamboru Ngala, bayan da yakai wata ziyarar aiki ta kwanaki uku.
Rahotonni sun bayyana cewa anyi musayar wutar da misalin ƙarfe 12:50 na rana zuwa 1:30.
Gwamnan ya zagaya ta wasu ƙananan hukumomin jihar sakamakon hare-haren da ‘yan ta’addan suka kai musu, sai dai babu tabbas ko gwamnan na cikin ayarin motocin.
Wata majiya da ke cikin tawagar ta tabbatar wa da wakilin Daily trust, faruwar lamarin a wata tattaunawa ta wayar tarho.