Dangote ne baƙar fatar da yafi Kowanne a cikin shekaru 300—Kashim Shettima

0
443

Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, yace daga shekara 300 da suka wuce zuwa yanzu ba’a samu mutum baƙar fata da yayi fice a duniya kamar Ali Dangote ba.

Shettima, ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin da yake jawabi a wajen taron masu zuba hannun jari na ƙasa da ƙasa daya gudana a jihar Taraba, wanda aka yiwa laƙabi da TARAVEST.

A ranar talata data gabata ne mujallar TIME Magazine, ta saka sunan Ali Dangote, a cikin mutane 100 masu ƙarfin arziki a faɗin duniya.

Dangote, shine mutum ɗaya tilo daga Najeriya, wanda ya samu damar shiga sahun mutane 100 masu ƙarfin arzikin duniya a shekarar 2025.

Shettima, ya yabawa Dangote, akan yadda ya jajirce wajen samar da matatar man fetur, yana mai cewa hakan kishin ƙasa ne da son cigaban a’lumma, tare da ƙirƙirar ayyukan yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here