Jam’iyyar APC na gudanar da wani muhimmin taro, a fadar shugaban ƙasa, wanda shine irin sa na farko, tun bayan da shugaban ƙasa Tinubu ya hau karagar mulki a shekarar 2023.
Taron yazo a daidai lokacin da shugaban ƙasar ke shirin cika shekaru 2 akan mulkin Najeriya, a ranar 29 ga watan Mayu.
Mahalarta taron na yau Alhamis, sun haɗar da Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, Kashim Shettima sai shugabannin Majalisun dokokin ƙasa da mataimakansu, da kuma gwamnonin jam’iyyar.
Taron yazo a daidai lokacin da ƴan jam’iyyar adawa ke tururuwar komawa APC a faɗin Najeriya.