Wasu ma’aikatan ofishin Jakadancin Isra’ila su biyu dake birnin Washington na Amurka, sun gamu da ajalin su yayin da suke fita daga wani gidan tarihin Yahudawa.
Wata majiya tace waɗanda aka kashe ɗin sun kasance ma’aurata.
Shugabar ƴansandan Washington Pamela Smith, ta ce an kama wani mutum mai suna Elias Rodriguez, wanda ya tunkari waɗanda lamarin ya rutsa da su tare da buɗe musu wuta.
Wani da abun ya faru a gaban idonsa ya ce mutumin ya yi ta ihun neman yancin Falasɗinawa, yana cewa ya yi hakan ne don nuna goyon baya ga mutanen Gaza.
Babbar Lauyar gwamnatin Amurka Pam Bondi, wadda ofishinta ke kusa da wajen, ta ce ta fito da gudu don ta ga me ke faruwa, kuma abun da ta tarar ya munana, kamar yadda ta ce.