Gwamnatin jihar Bayelsa ta dakatar da masaraucin gargajiya Wilcox Seiyefa, dake yankin Swali, na ƙaramar hukumar Yenagoa.
Gwamnatin tace dakatarwar ta nan take ce, kamar yadda Kwamishinar yaɗa labarai ta Bayelsa Ebiuwou Koku-Obiyai, ta sanar a ranar Laraba.
Sanarwar da Kwamishinar ta fitar ta kara da cewa an dakatar da Wilcox Seiyefa, sakamakon yadda ya kasa magance matsalolin ayyukan ɓata gari da aikin ƙungiyoyin asiri a yankin Swali.
Gwamna Douye Diri, ne ya amince da dakatarwar, inji Ebiuwou Koku-Obiyai.