A’lummar Bagega da Kawaye, dake ƙaramar hukumar Anka, sun ɗauki matakin nemarwa kansu zaman lafiya ta hanyar kulla yarjejeniya da kungiyoyin ƴan fashin daji, musamman a wannan lokaci da damuna ta fara sauka.
Mutanen sun ɗauki wannan mataki don samarwa kansu zaman lafiya, bayan sunyi zargin cewa gwamnati ta gaza fitar da su daga cikin ƙalubalen rashin tsaro.
Rahotonni sun bayyana cewa kusan makonni uku aka shafe a’lummar wadannan yankuna na fuskantar hare haren yan bindiga a yankin Bagega, wanda hakan ya haifar da koma bayan harkokin kasuwanci da tattalin arzikin mutanen yankin. Hakan ya janyo rufe kasuwanni da yin garkuwa da mutane, bayan kisan wasu da dama.
Sai dai wata majiya tace duk da wannan yanayi sau ɗaya jami’an tsaro suke yin atisaye a yankin cikin kowane mako guda, wanda ake ganin kamar bawa ƴan ta’addan dama suyi abinda suke so ne.
Mazauna Bagega, sun ce suna cikin damuwa saboda sansanin yan bindiga ya mamaye su, saboda kilomita 15 ce ta raba gidajen su da sansanin ƴan fashin.
Haka ne yasa mutanen suka nemi Sarkin Anka ya basu damar yin yarjejeniyar kai tsaye da ɓata garin don gujewa hare haren su da yin garkuwa da mutane.
Kamar yadda jaridar Solacebase, ta rawaito, Sarkin Anka ya bawa a’lummar damar yin yarjejeniya da yan ta’addan sai dai shi bai shiga cikin tattaunawar ba, saboda gwamnatin Zamfara bata goyon bayan hakan.
Dama ƴan fashin daji sun saba kaiwa manoma hari a irin wannan lokaci da bayan damuna.