Rundunar ƴan sandan ƙasa reshen jihar Jigawa, ceto wata tsohuwa mai kimanin shekaru 80 da aka yi garkuwa da ita a gidanta da ke ƙaramar hukumar Minjibir ta jihar Kano.
Kakakin Rundunar SP Lawan Adam, ya ce mutanen da suka yi garkuwa da tsohuwar sun ɓoye ta a cikin wani dajin Jigawa, bayan ɗauke ta daga Kano.
Yace bayan sace tsohuwar, barayin sun tafi da ita wasu dazukan da ke tsakanin ƙananan hukumomin Garki da Sule Tankarkar, inda daga nan ne jami’an su tare da haɗin gwiwar ƴan bijilanti suka farwa maharan, tare da ceto ta.
Kakakin ƴan sandan ya ƙara da cewa jami’ansu sun yi nasarar kama wasu ƴan fashin daji biyar da aka jima ana neman su.
Daga cikin makaman da aka kwato a wajen ƴan fashin akwai bindigogi irar AK-47 guda biyu, da ƙirar GPM guda ɗaya sai wayoyin hannu da kuma babura.