A’lummar Jalingo babban birnin jihar Taraba, sun bayyana farin ciki akan yadda suka fara samun wutar lantarki ta tsawon awanni 24, ba tare da ƙiftawa ba, gabanin wata ziyarar aiki da shugaban ƙasa Tinubu ya shirya kai musu.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN, ya rawaito cewa shugaban ƙasa Tinubu ya sanya mataimakin sa, Kashim Shettima, a matsayin wanda zai wakilce shi a ziyarar buɗe shirin zuba hannun jari na ƙasa da ƙasa a jihar Taraba, wanda aka yiwa laƙabi da TARAVEST, 2025.
Wani mazaunin garin mai suna Donald Musa, ya bayyana samun lantarkin babu daukewa a matsayin wani ba zata, sannan yayi fatan za’a cigaba da basu tsayayyar wuta har bayan ziyarar ta gwamnatin tarayya.
Haka zalika wata mai yin rayuwa a birnin Jalingo, mai suna Maimuna Abubakar, cewa tayi kafin yanzu wutar da suke samu bata wuce ta awanni 4 a kowace rana, sai dai a yanzu da akace shugaban ƙasa zai zo suna samun wuta ba tare da ƙiftawa ba.
NAN yace akwai fitattun mutane da ake sa ran zasu halarci taron irin sa na farko a jihar Taraba, wanda kawo yanzu mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, da Atiku Abubakar, sun sauka a wajen taron.