Za’a binciko dalilan kaiwa a’lummar Filato hare-hare—Mutfwang

0
128

Gwamnan Jahar Filato, Caleb Mutfwang, ya kafa wani kwamiti mai ɗauke da mutane 10, wanda zai yi aikin binciken hare-haren da ake ta fama da su a jahar.

An ƙaddamar da kwamitin ne a Jos, kuma an bawa mutanen aikin gano adadin al’ummomin da aka kai wa hari tun daga shekarar 2001 zuwa yanzu, yawan mutanen da suka mutu, irin ɓarnar da aka yi, da kuma waɗanda ake zargin suna da hannu a lamarin.

Gwamna Mutfwang ya ce manufar kwamitin ita ce gano musabbabin matsalolin tsaro da kuma bayar da shawarwari domin samun zaman lafiya mai ɗorewa a Filato.

Shugaban kwamitin, Manjo-Janar Rojas Nicholas (mai ritaya), ya ce za su yi aiki da adalci da gaskiya domin fitar da rahoto mai inganci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here