Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya yi karin haske kan yadda aka riƙa gudanar da harkokin siyasa a bayan fage a farkon gwamnatin marigayi tsohon shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’adua, musamman yadda ya shawarci Yar’adua da yayi taka tsantsan akan yadda zai tafiyar da mu’amalar sa da tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo, wanda yake a matsayin uban gidan Yar’adua na siyasa.
A cikin littafin rayuwar sa daya ƙaddamar a ranar 13 ga watan Mayu Sule Lamido, ya bayyana wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a siyasar Najeriya.
A shafin littafin na 257, tsohon gwamnan yayi taza da tsifa akan yadda rikicin siyasa ya faro tsakanin Yar’adua da Obasanjo, wanda yace ka’iya kawo babban hargitsi a fannin siyasa in ba’a tabawa rikicin birki ba.
Yace akwai wani batun aikin wutar lantarki da aka tattauna a majalisar dokokin ƙasa na kusan dala biliyan 16, a zamanin mulkin Yar’adua, da hakan ke nuna kamar so ake a bayyana wasu abubuwan da suka faru marasa kyau a zamanin mulkin Obasanjo.
A yayin tattaunawa akan batun aikin wutar lantarkin ƴan Najeriya na ganin cewa Obasanjo ne ya sace Dala biliyan 16 na samar da lantarkin, wanda daga nan ne na janyo hankalin Yar’adua akan yadda ake kallon binciken da aka faro na tattaunawa akan batun aikin wutar da cewa zai kawo rashin fahimta tsakanin sa da Obasanjo, inji Lamido.
Sule Lamido, yace shine ya zube a kasa yana mai neman dan girman Allah Yar’adua yayi hakuri kar yayi rigima da Obasanjo.