Hukumar dake kula da gidajen gyaran hali ta ƙasa, ta ce ta ƙaddamar da bincike tare da neman wasu fursunoni bakwai da suka tsere daga gidan gyaran hali dake Ilesa a Jahar Osun, bayan ruwan sama mai ƙarfi ya rushe katangar gidan.
Mai magana da yawun hukumar, Umar Abubakar, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar da daren Talata.
Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 2 na daren Talata.
Sanarwar tace bayan faruwar lamarin, shugaban hukumar kula da gidajen gyaran hali ta ƙasa, Sylvester Ndidi Nwakuche, ya bayar da umarnin gaggauta gudanar da bincike kan yadda fursunonin suka samu damar guduwa da kuma daukar matakin kamo su.
Sanarwar ta ƙara da cewa hukumar tana aiki kafada da kafada da sauran hukumomin tsaro da shugabannin al’umma domin kamo waɗanda suka tsere tare da mayar da su gidan yarin.