Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano kara soke lasisin gidajen wasan gala 8

0
102

Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano kara soke lasisin gidajen wasan gala 8 

Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta Jahar Kano karkashin jagorancin Alhaji Abba El-mustapha ta soke lasisin wasu gidajen wasannin gala har guda 8 bisa samun su da laifin karya dokokin ta.

A wata sanarwa da jami’an yada labaran Hukumar Abdullahi Sani Sulaiman ya fitar Jim kadan bayan kammala taron da manya jami’in Hukumar.

Abdullahi Sani Sulaiman ya bayyana cewa gidajen wasannin da aka rufe sun hada da

1. HAMDALA ENTERTAINMENT (Ungoggo)

2. LADY J ENTERTAINMENT (SanyaOlu)

3. DAN HAUSA ENTERTAINMENT (Sanya Olu)

4. NI’IMA (Zungeru)

5. ARIYA ENTERTAINMENT ( Abedi sabon gari)

6. BABBANGIDA ENTERTAINMENT (Balatus)

7. HARSASHI ENTERTAINMENT ( Ebedi sabon gari)

8. WAZOBIYA (Sanya Olu)

Abdullahi Sani ya Kara da cewa doka ce ta bawa Hukumar damar saka ido tare da tabbatar da masu gidajen wasanni basu ketare iyaka ba inda ya bayyana cewa dokar ta kara bawa Hukumar damar ladaftar da duk wani gida ko dan wasa data samu da aikata laifi.

Idan ba’a mantaba a kwanakin baya Hukumar tayi gargadi tare da dakatar da wasu gidajen wasannin gala tare da soke lasisin wasu daga cikinsu biyo bayan samun su da laifi.

Abba El-mustapha ya yi kira ga jami’an tsaro dasu cigaba da bawa Hukumar hadin Kai sau da kafa domin tabbatar da ana bin doka yadda ya kamata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here