Mahukuntan dake ƙarƙashin kulawar Hamas a fannin bayar da agajin gaggawa sun ce wasu hare haren sama da Isra’ila ta kaiwa yankin Gaza sunyi sanadiyar mutuwar mutane 15, yayin harin da takai a tsakar dare.
Harin da aka kai a yankin Jabalia, dake arewacin Gaza ya kuma jikkata karin mutane 13.
Wani harin na da ban kuma ya kashe mutane biyu da karamin yaro ɗaya.