An samu Hamdiyya Sidi Shariff, a babban asibitin Bakura dake jihar Zamfara.
Lauyan dake kare ta a shari’ar dake gudana tsakanin ta da gwamnatin jihar Sokoto, akan zargin tayar da zaune tsaye, Abba Hikima, ne ya sanar da hakan a shafin sa na Facebook.
Sai dai yace akwai jami’an tsaro a tare da ita, inda yace ta tabbata sace ta aka yi.
Hamdiyya dai ta bace tun a jiya Talata, Lokacin da ta fita siyan kayan miya da misalin karfe 10 na safe, gabanin lokacin da za’a cigaba da yin Shari’a tsakanin ta da gwamnatin Sokoto.