An rasa inda Hamdiyya Sidi Shariff, ta shiga a jihar Sokoto

0
184

An nemi Hamdiyya Sidi Sharrif, an rasa wadda itace Gwamnatin Jihar Sokoto ke shari’a da ita kan zargin yunkurin tada zaune tsaye a jihar.

Lauyan dake kare Hamdiyya,  Abba Hikima Fagge, ne ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook, inda ya ce ta bace tun a jiya Talata, Lokacin da ta fita siyan kayan miya da misalin karfe 10 na safe, kuma ba a sake ganin ta ba har zuwa wannan loakci.

A yau ne ake sa ran za a ci gaba da sauraren karar su da Gwamnatin Jihar Sokoto, sai dai lauyan ya ce tuni suka sanar da rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto game da lamarin É“acewar tata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here