Ƴan siyasa da sojoji na taimakon Boko Haram da bayanan sirri–Zulum

0
205

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum, yayi zargin cewa akwai yan siyasa da sojojin dake yiwa ƴan ta’addan Boko Haram leƙen asiri da kuma haɗa kai dasu.

Zulum, ya sanar da hakan a yau Laraba lokacin da yake ganawa da manema labarai, yana mai bugun ƙirgin cewa gwamnatin jihar zata saka ƙafar wando ɗaya da duk masu yiwa harkokin tsaro zagon ƙasa.

Tabbas muna da yan siyasa da jami’an soji da sauran al’ummar gari dake taimakawa Boko Haram, da bayanan sirri, kuma zamu dauki mataki akan su, inji Zulum.

A cikin watanni 6 zamu iya kawo karshen wannan matsalolin da muke ciki, na hauka. Akwai bukatar mu dena siyasantar da sha’anin tsaro, a cewar gwamnan.

Daga bangare guda Zulum, yayi zargin cewa jami’an tsaron Najeriya basu da kayan aiki da kwarewa irin ta mayaƙan Boko Haram, sannan yace sojojin kasar nan basu da kayan aikin da zasu iya kawo karshen rashin tsaron da ake ciki.

Sannan ya kara da cewa sojoji kaɗai ba zasu iya magance matsalolin tsaron da Najeriya ke ciki ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here