Wasu maharan da ake zaton yan fashin daji ne sun kashe mutane 19 tare da ƙone gidaje da shagunan mutane a kauyen Gobirawa dake mazaɓar Kuki dake karamar hukumar Dutsinma.
Rundunar ƴan sandan Katsina, ta tabbatar da kai harin ta bakin kakakin DSP Abubakar Sadiq, inda yace mutane 5 aka kashe sannan aka ƙone ababen hawa 2. Ya kuma ce an fara gudanar da bincike don gano maharan don hana afkuwar irin hakan a nan gaba.
Sai dai mazauna garin da aka kaiwa harin sun tabbatar da cewa mutanen da yan ta’addan suka kashe sun kai 19, a harin na daren ranar Asabar data gabata, wanda akace maharan sun fito daga dajin Danmusa.
Wani da lamarin ya faru a gaban idon sa yace harin ya rutsa da mata da ƙananun yara, sannan wasu sun mutu a lokacin da suke gudun tsira da rayuwar su.
Yace an ƙone gidaje fiye da 20 tare da sace kayan kowanne shagon garin da kuma ƙone su.