Sabon Shekau yayi barazana ga malaman addini da jami’an tsaro

0
197

An samu wani kwamandan kungiyar ƴan ta’addan Boko Haram, da ya ayyana kansa a matsayin sabon Shekau, sannan ya fara yin gargadi ga jami’an tsaro, malaman addinin Islama da sauran al’ummar dake goyon bayan gwamnati akan yaƙi da ƴan ta’adda.

Barazanar tazo bayan da hafsan hafsoshin tsaron ƙasa Janar Christopher Musa, ya nemi ƴan ta’adda su miƙa wuya ga jami’an tsaro ko su gane kuren su.

A wani sabon faifan bidiyo da kafar yada labarai ta PRNigeria ta samu kuma ta fassara daga Hausa zuwa turanci, sabon Shekau, ya tsawatarwa da Janar Christopher Musa, da rundunar sojin ƙasa akan suyi watsi da yaƙi da ƴan ta’addan da suke yi.

Ya yi ikirarin cewa, kamar magabatan sa, Musa ba zai yi nasarar murkushe Boko Haram ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here