Kungiyar maʼaikatan lantarki shiyyar Kano da suka hada da jihohin Kano, Jigawa da Katsina sun ce za su shiga yajin aiki daga karfe 12 na daren Talatar nan.
Kafar yaɗa labarai ta Arewa Updates, ta rawaito cewa babban Sakataren Tsare-tsaren kungiyar Comr. Muhammad Babangida Muhammad ne ya sanar da hakan da maraicen Talatar nan.
Ya ce, za su shiga yajin aikin ne saboda gazawar kamfanin KEDCO na biyan kudin fanshon maʼaikata.