Hukumomin Saudiyya sun kama iyalan ɗan bindiga Ado Aliero

0
233

Hukumomin Saudiyya sun samu nasarar kama wasu mata biyu da ake kyautata zaton ɗaya cikinsu ita ce mahaifiyar Ado Aliero, ce wanda ya kasance rikakken shugaban wasu yan bindigar da suka addabi al’umma a arewacin Najeriya.

Rahotanni sun ce matan biyu da aka kama, sun haɗa da mata da kuma mahaifiyar Ado Aliero, waɗanda suka isa Madina domin sauke farali.

 Aliero na ɗaya daga cikin ƴan ta’addan da suka yi ƙaurin suna wajen garkuwa da mutane domin karbar diyya da kuma munanan hare hare a yankin arewa maso yammacin ƙasar nan. 

Rahotanni sun ce yanzu haka hukumomin ƙasar nan na aiki tare da na Saudiya domin tasa keyar waɗannan mutane biyu zuwa gida. 

Kama waɗannan dangi na shi na zuwa ne kwana guda bayan kama wani mai garkuwa da mutanen da jami’an tsaro suka yi a Abuja, a daidai lokacin da ake tantance maniyata Hajji bana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here