A wani mataki na tabbatar da bin ka’idoji tare da inganta sana’ar masu sayar da maganin gargajiya a Kano tare da masana’antar Kannywood, Hukumar Tace Fina-finai Dab’i ta Jihar Kano karkashin jagorancin Abba El-mustapha ta dakatar da duk wani nau’in tallace-tallacen maganin gargajiya a cikin fina-finai ko masu yawo a tituna da lasifika.
Wata sanarwar da jami’in yaÉ—a labarai na hukumar Abdullahi Sani Sulaiman, tace shugaban Hukumar, Abba El-Mustapha ne ya bayyana cewa yawancin tallace-tallacen da ake yi a tituna da lasifika ko kuma a cikin Fina-finan na karya dokokin Hukumar, wadanda ke bukatar a tace su kafin a fitar da su ga jama’a.
Abba El-Mustapha ya bayyana hakan ne a ofishinsa yayin wata ganawa ta musamman da manema labarai.
A saboda haka Hukumar na umartar duk masu tallan Maganin gargajiya a tituna da lasifika tare da cikin fina-finai da su miko tsarin tallace tallacen Maganinsu domin tantancewa tare da samun sahalewar Hukumar a cikin mako daya tun daga Laraba 21 Ga Mayu, 2025 domin kaucewa daukar matakin doka.
El-Mustapha ya kuma yi kira ga dukkanin tashoshin talabijin tare da Hukumar Kula da kafafen yada Labarai ta Kasa (NBC) da su goyi bayan kokarin da hukumar ke yi dan tabbatar da a na bin dokar Hukumar domin inganta tarbiyya a tsakanin al’ummar Kano.