Gwamnatin jihar Kaduna, karkashin jagorancin Gwamna Uba Sani, ta bayar da tallafin motocin aikin samar da tsaro guda 150 da kuma babura 500, ga hukumomin tsaro don inganta ayyukan su jami’an tsaro da fatattakar yan ta’adda.
Gwamna Uba Sani, ne ya Æ™addamar da bayar da tallafin motoci da baburan, yana mai cewa an yi hakan da manufar inganta sintirin jami’an tsaro a fadin jihar Kaduna.
Jihar Kaduna, dai na daga cikin jihohin arewa masu fama da matsalolin rashin tsaro, da suka ƙunshi garkuwa da mutane don karɓar kuɗin fansa, kisan kai da sauran su.